2 Kings 16:17 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sarkin Ahaz ya kawar da katakon ya kuma ɗauke tasoshin daga mazauninsu da ake iya matsarwa. Ya ɗauke ƙaton kwano mai suna Teku daga kan bijiman tagullar da ya tallafe su ya ajiye a kan mazaunin dutse.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ سَرْكِے أَهَظْ يَيَنْكٜىٰ ڢَلّٜىٰنْ كُواْوَنٜىٰ غٜىٰڢٜىٰ نَأَمَلَنْكٜىٰنْ، سَيْ يَڢِتَرْدَ مَنْيَنْ ݣُونُواْنِنْ؞ سَيْ يَثِرٜىٰ ڧَتُوانْ ݣُونُواْ وَنْدَ عَكٜىٰكِرَنْسَ تٜىٰكُ وَنْدَ يَكٜىٰ ذَمَ عَكَنْ صِڢُّواْڢِنْ بِجِمَيْ نَڧَرْڢٜىٰنْ تَغُلَّ، يَأَجِيٜىٰشِ عَكَنْ دَٻٜىٰنْ دُوَڟُو؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sarki Ahaz kuwa ya yanke sassan dakalan, ya ɗauke daruna da suke bisansu, ya kuma ɗauke kwatarniya da take bisa bijimai na tagulla, ya ajiye kwatarniya a daɓen dutse.