2 Kings 16:5 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Rezin sarkin Aram, da Feka ɗan Remaliya sarkin Isra’ila suka haura don su kai wa Urushalima hari, suka kuma kewaye Ahaz, amma ba su iya shan ƙarfinsa ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَرْكِے رٜىٰظِنْ نَ سُورِيَ دَ سَرْكِے ڢٜىٰكَ طَنْ رٜىٰمَلِيَ نَ إِسْرَٰٓءِيلَ سُكَ كَٰوُاْ يَاڧِ عَكَنْ عُرُوشَلِيمَ؞ سُكَ كٜىٰوَيٜىٰتَ، عَمَّا بَسُ عِيَ ثِنْ سَرْكِے أَهَظْ دَ يَاڧِبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Rezin Sarkin Suriya kuwa, da Feka ɗan Remaliya Sarkin Isra'ila, suka kawo wa Urushalima yaƙi. Suka kewaye Ahaz da yaƙi, amma ba su ci shi ba.