2 Kings 16:7 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ahaz ya aika a faɗa wa Tiglat-Fileser sarkin Assuriya cewa, “Ni abokin tarayyarka ne kuma mai dogara da kai. Ka haura ka cece ni daga hannun sarkin Aram da hannun sarkin Isra’ila waɗanda suke kawo mini hari.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَرْكِے أَهَظْ يَعَيْكَ دَ یَنْ عَيْكَ ذُوَاغَ سَرْكِے تِغْلَتْ ڢِلٜىٰسٜىٰرْ نَڧَسَرْ أَسُّرِيَ؞ يَثٜىٰ «نِے بَاوَنْكَ نٜىٰ، طَنْكَ كُمَ؞ بَرِ كَهَوْرُواْ نَنْ كَكُٻُتَرْ دَنِے دَغَ حَنُّنْ سَرْكِنْ سُورِيَ دَ نَ إِسْرَٰٓءِيلَ وَطَنْدَ سُكٜىٰ كَٰوُاْ مِنِ يَاڧِ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ahaz kuwa ya aiki manzanni wurin Tiglat-filesar, mai mulkin Assuriya, ya ce, “Ni baranka ne, ɗanka kuma, ka zo ka cece ni daga hannun Sarkin Suriya da Sarkin Isra'ila, waɗanda suke yaƙi da ni.”