2 Kings 16:9 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai sarkin Assuriya ya ji roƙonsa. Ya tashi ya fāɗa wa Damaskus da hari ya kuma kame ta. Ya kwashi mazaunanta zuwa Kir, ya kuma kashe Rezin.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ سَرْكِنْ أَسُّرِيَ يَجِ ضُواْڧُوانْسَ؞ يَتَاشِ يَڢَاطَوَ دِمَشْڧُ دَ يَاڧِ، يَكُوَ ثِتَ؞ يَكَشٜىٰ سَرْكِے رٜىٰظِنْ يَكُمَ ݣُوشِ مُتَنٜىٰنْ دِمَشْڧُ ذُوَا بَوْتَا عَڧَسَرْ كِرْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Tiglat-filesar ya ji roƙonsa, sai ya zo ya faɗa wa Dimashƙu da yaƙi, ya ci ta. Sa'an nan ya kwashe mutane zuwa Kir. Ya kuma kashe sarki Rezin.