2 Kings 17:15 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Suka yi watsi da farillansa da yarjejjeniyar da ya ƙulla da kakanninsu, da kuma kashedin da ya yi musu. Suka bi gumaka marasa amfani, wannan ya sa su ma kansu suka zama marasa amfani. Suka kwaikwayi sauran ƙasashen da suke kewaye da su, ko da yake Ubangiji ya umarce su cewa, “Kada ku yi rayuwa irin tasu,” suka kuwa yi abin da Ubangiji ya hana su.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سُكَ ڧِ ڧَٰعِدُواْدِنْسَ دَ يَرْجٜىٰجٜىٰنِيَرْ دَ يَيِ دَ كَاكَنِّنْسُ دَ كُمَ غَرْغَطِنْسَ؞ سُكَبِے غُمَكَنْ بَنْظَ، سَيْ سُكَ ذَمَ بَنْظَ؞ سُكَ كُمَبِے أَلْعَادُنْ ڧَبِيلُنْ دَسُكٜىٰ كٜىٰوَيٜىٰ دَسُو، كُواْدَيَكٜىٰ يَهْوٜىٰهْ يَا عُمَرْثٜىٰسُ ثٜىٰوَ كَدَ سُكُواْيِ رَايُوَرْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Suka yi watsi da dokokinsa, da alkawarinsa da ya yi wa kakanninsu, da kuma faɗakarwar da ya yi musu. Suka bi gumakan banza, suka zama banza, suka bi halin al'ummai da suke kewaye da su, waɗanda Ubangiji ya umarce su kada su yi kamarsu.