2 Kings 17:16 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Suka wofinta dukan umarnan Ubangiji Allahnsu, suka yi wa kansu gumakan zubi na siffar ’yan maruƙa biyu, da kuma ginshiƙin Ashera. Suka rusuna wa rundunan taurari, suka kuma yi wa Ba’al sujada.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ كُمَ سُكَڧِ عُمَرْنَنْ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْسُ؞ سُكَيِ صِڢُّواْڢِنْ ظُبِے نَیَنْ بِجِمَيْ بِيُ دَ كُمَ غُنْكِنَّنْ أَشٜىٰرَ دُواْمِنْ كَنْسُ؞ مُتَنٜىٰنْ سُكَيِ سُجَّدَ غَ رَانَ دَ وَتَ دَ تَوْرَرِنْ سَمَ، سُكَ كُمَيِ وَ بَعَلْ سُجَّدَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Suka bar dukan umarnan Ubangiji Allahnsu, suka yi wa kansu siffofin zubi na 'yan maruƙa biyu, suka yi gunkiyan nan, Ashtoret, suka yi wa taurari sujada, suka bauta wa Ba'al.