2 Kings 17:24 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sarkin Assuriya ya kawo mutane daga Babilon, Kuta, Afa, Hamat da Sefarfayim ya zaunar da su a garuruwan Samariya don su maya gurbin Isra’ilawa. Suka mallaki Samariya suka kuma zauna a garuruwansu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَرْكِنْ أَسُّرِيَ يَݣُوشِ مُتَنٜىٰ دَغَ بِرَنٜىٰنْ بَابِيلَ دَ نَ كُتَ دَ أَوَّ دَ هَمَتْ دَ سٜىٰڢَرْوَيِمْ يَذَوْنَرْ دَسُو عَثِكِنْ غَرُرُوَ نَ سَمَرِيَ، أَوُرَارٜىٰنْدَ يَڢِتَرْدَ مُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ؞ مُتَنٜىٰنَّنْ سُكَ كَرْٻِ ڧَسَرْ سُكَ ذَوْنَ عَبِرَنٜىٰنْتَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sarkin Assuriya kuwa ya kawo mutane daga Babila, da Kuta, da Awwa, da Hamat, da Sefarwayim, ya zaunar da su a garuruwan Samariya a maimakon jama'ar Isra'ila. Sai suka mallaki Samariya, suka zauna a garuruwanta.