2 Kings 18:10 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A ƙarshen shekara ta uku, Assuriyawa suka ci Samariya da yaƙi. An ci Samariya da yaƙi a shekara ta shida ta mulki Hezekiya, wanda ya zo daidai da shekara ta tara ta mulkin Hosheya sarkin Isra’ila.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَايَنْ شٜىٰكَرَا عُكُ سَيْ شَلْمَنٜىٰظٜىٰرْ يَڨُوثٜىٰ بِرْنِنْ سَمَرِيَ؞ وَنَّنْ يَڢَرُ أَ شٜىٰكَرَا تَشِدَ تَمُلْكٍ سَرْكِے هٜىٰزٜىٰكِيَ، وَتُواْ شٜىٰكَرَا تَتَرَ تَمُلْكٍ سَرْكِے هُواْشٜىٰيَ نَ إِسْرَٰٓءِيلَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A ƙarshen shekara ta uku, ya ci ta da yaƙi. A lokacin Hezekiya yana da shekara shida da sarauta, Hosheya kuwa yana da shekara tara da tasa sarauta.