2 Kings 18:4 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ya kawar da masujadan kan tudu, ya farfasa keɓaɓɓun duwatsu, ya sassare ginshiƙan Ashera. Ya fashe macijin tagullan da Musa ya yi, gama har zuwa lokacin nan Isra’ilawa suna ƙona turare gare shi. (An ba shi suna Nehushtan.)
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَرُرُّشٜىٰ وُرَارٜىٰنْ سُجَّدَ دَ بَسُ دَاثٜىٰبَ دَ دُووَڟُنْ سُجَّدَ دَ غُمَكَنْ أَشٜىٰرَ؞ يَڢَرْڢَشٜىٰ مَثِيجِ نَڧَرْڢٜىٰنْ تَغُلَّرْ نَنْ دَ مُوسَٰى يَيِ، وَنْدَ سُكَ بَاشِ سُونَ نَهُشْتَنْ؞ سَرْكِے هٜىٰزٜىٰكِيَ يَيِ وَنَّنْ غَمَا حَرْ ذُوَا ݣُونَكِنَّنْ مُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ سُنَ ڧُواْنَ وَ مَثِيجِنْ هَدَايُ نَتُرَارٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya kawar da wuraren tsafi na kan tuddai, ya rurrushe ginshiƙai, ya sassare siffar Ashtoret. Ya kuma farfashe macijin tagulla wanda Musa ya yi, gama har zuwa lokacin jama'ar Isra'ila suna miƙa masa hadaya ta turaren ƙonawa. Aka ba macijin suna Nehushatan.