2 Kings 18:9 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A shekara ta huɗu ta Hezekiya, wato, shekara ta bakwai ke nan ta mulkin Hosheya ɗan Ela sarkin Isra’ila; Shalmaneser Sarkin Assuriya ya tasam ma Samariya da yaƙi; ya kewaye ta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَ شٜىٰكَرَا تَهُطُ تَمُلْكٍ سَرْكِے هٜىٰزٜىٰكِيَ نَ يَهُودَ، وَدَّ عِتَثٜىٰ شٜىٰكَرَا تَبَݣَويْ تَمُلْكٍ سَرْكِے هُواْشٜىٰيَ طَنْ عٜىٰلَ نَ إِسْرَٰٓءِيلَ، سَيْ سَرْكِے شَلْمَنٜىٰظٜىٰرْ نَ أَسُّرِيَ يَكَٰوُاْ يَاڧِ عَكَنْ إِسْرَٰٓءِيلَ أَ سَمَرِيَ، يَكُوَ كٜىٰوَيٜىٰ بِرْنِنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A shekara ta huɗu ta sarautar sarki Hezekiya, a lokacin Hosheya ɗan Ila, Sarkin Isra'ila, yana da shekara bakwai da sarauta, sai Shalmanesar Sarkin Assuriya ya kawo wa Samariya yaƙi, ya kewaye ta.