2 Kings 19:23 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ta wurin manzanninka ka tara wa Ubangiji zagi. Ka kuma ce, “Da yawa kekunan yaƙina na haye kan ƙwanƙolin duwatsu, wurin mafi tsawo na Lebanon. Na sassare itacen al’ul nasa mafi tsawo mafi daraja na itacen fir nasa. Na ratsa har can tsakiyar kurmi, mafi kyau na kurminsa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
تَیَنْ عَيْكَنْكَ كَيِ وَ عُبَنْ‌غِجِ غُواْرِ؞ كَثٜىٰ تَيَوَنْ كٜىٰكُنَنْ يَاڧِنْكَ، كَاهَوْ كَنْ تُدَّيْ مَڢِے ڟَيِ، حَرْ إِيَاكَرْ ڟَوُانْ تُدَّنْ لٜىٰبَنُوانْ؞ كَاݣُونْتَرْ دَ عِتَتُوَنْ سٜىٰدَ مَڢِے ڟَيِ، دَ عِتَتُوَنْ ڢِرْ مَڢِے ݣَوْ؞ كَاثٜىٰ كَاكَيْ إِيَاكَرْ تُدَّنْ لٜىٰبَنُوانْ، كَاشِغَ ثِكِ ثِكِنْ كُرْمِنْتَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ka aiki manzanninka su nuna mini girmankai saboda ka ci duwatsu mafi tsayi da karusanka, har ma ka ci duwatsun Lebanon. Ka yi fariyar a kan ka datse itatuwan al'ul mafi tsayi da na fir, har kuma ka shiga har can tsakiyar kurmi.