2 Kings 19:26 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ƙarfin mutanensu ya tsiyaye, suka razana aka kuma kunyata su. Suna kama da tsirai a gona, kamar sabon toho kamar ciyawa mai tohuwa bisa rufin ɗaki wanda ya bushe saboda zafi, kafin yă yi girma.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَدَّ مَذَوْنَنْ بِرَنٜىٰنْ ذَاسُ رَسَ ڧَرْڢِے، ذَاسُجِڟُواْرُواْ سُضِكِثِے، سُذَمَ كَمَرْ ثِيَوَ أَدَاجِ، كَمَرْ ڧأَنَانً غَنْيَيٜىٰ، كَمَرْ ڟِرُواْ عَكَنْ رُڢِنْ طَاكِ، وَنْدَ إِسْكَ تَبُوشٜىٰ كَاڢِنْ يَيِ غِرْمَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Mazauna cikinsu suka rasa ƙarfi, suka damu, suka ruɗe. Suka zama kamar ciyawar saura, ko kuma ciyawar da ta tsiro a rufin soro, da iskar gabas mai zafi ta busa, har ta bushe.