2 Kings 19:29 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Wannan zai zama alama a gare ka, ya Hezekiya, “Bana, za ku ci amfanin gonar da ya tsira da kansa, baɗi kuma amfanin gonar da ya tsiro daga na bara. Amma a shekara ta uku, za ku yi shuki, ku kuma girbe, ku dasa gonakin inabi, ku kuma ci ’ya’yansa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ عِشَايَ يَثٜىٰ وَ هٜىٰزٜىٰكِيَ، «غَا أَبِنْدَ ذَيْ ذَمَ مَكَ عَلَمَ؞ أَوَنَّنْ شٜىٰكَرَا ذَاكُثِ دَغَ أَبِنْدَ يَڟِيرَا دَ كَنْسَ؞ أَ شٜىٰكَرَا تَبِيُنْ كُمَ ذَاكُثِ أَبِنْدَ يَڟِيرَا دَغَ نَشٜىٰكَرَا تَڢَرْكُوانْ؞ عَمَّا أَ شٜىٰكَرَا تَ عُكُنْ، كُيِ نُواْمَ، كُيِ غِرْبِے، كُشُوكَ غُواْنَكِنْ إِنَبِے، كُثِ أَمْڢَانِنْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan Ishaya ya ce wa sarki Hezekiya, “Wannan zai zama alama a gare ka. A wannan shekara za ku ci gyauro, a shekara ta biyu za ku ci gyauron gyauron, a shekara ta uku kuwa za ku shuka ku girbe, ku dasa inabi a gonakin inabi, ku ci 'ya'yansu.