2 Kings 19:37 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Wata rana yayinda yake sujada a haikalin Nisrok, allahnsa, sai ’ya’yansa maza, Adrammelek da Sharezer suka kashe shi da takobi, suka gudu zuwa ƙasar Ararat. Sai Esar-Haddon ɗansa ya gāje shi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَتَرَانَ يَايِنْ دَيَكٜىٰ سُجَّدَ أَطَاكِنْ غُنْكِنْسَ نِسْرُواكْ، سَيْ یَیَنْسَ مَظَا أَدْرَمّٜىٰلٜىٰكْ دَ شَرٜىٰظٜىٰرْ سُكَ كَشٜىٰشِ دَ تَكُواْبِے، سُكَ غُدُ ذُوَا ڧَسَرْ أَرَرَاتْ؞ سَعَنً وَنِ طَنْسَ مَيْ سُونَ عٜىٰسَرْهَدُّوانْ يَغَاجٜىٰشِ يَذَمَ سَرْكِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da yake yin sujada a haikalin gunkinsa Nisrok, sai 'ya'yansa, Adrammelek da Sharezer, suka kashe shi da takobi, sa'an nan suka tsere zuwa ƙasar Ararat. Sai ɗansa guda, wato Esar-haddon ya gāji gadon sarautarsa.