2 Kings 19:8 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da sarkin yaƙin ya ji cewa sarkin Assuriya ya bar Lakish, sai ya janye, ya kuma iske sarkin yana yaƙi da Libna.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَ وَكِيلِنْ سَرْكِے يَكُواْمَ، سَيْ يَغَمُ دَ سَرْكِنْ أَسُّرِيَ يَنَ يَاڧِ دَ لِبْنَ، غَمَا وَكِيلِنْ يَجِ لَابَرِ ثٜىٰوَ سَرْكِنْ يَا رِغَا يَا بَرْ بِرْنِنْ لَكِشْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Rabshake kuwa ya koma, ya tarar Sarkin Assuriya yana yaƙi da Libna, gama ya ji labari sarki ya riga ya bar Lakish.