2 Kings 2:15 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ƙungiyar annabawa daga Yeriko, waɗanda suke kallo, suka ce, “Ruhun Iliya yana a kan Elisha.” Sai suka je su tarye shi, suka rusuna har ƙasa a gabansa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَ ڧُنْ‌غِيَرْ أَنَّبَاوَنَّنْ سُكَ غَنِ حَكَ سَيْ سُكَثٜىٰ «إِيكُوانْ رُوحٌ إِلْيَاسُ يَنَ عَكَنْ أَلْيَسَعَ!» سُكَ تَڢِے وُرِنْسَ سُكَ رُسُنَ سُنْ غَيْشٜىٰشِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da annabawa hamsin da suke Yariko suka ga ya haye ya nufo su, sai suka ce, “Ai, ruhun Iliya yana kan Elisha.” Sai suka tafi su tarye shi, suka rusuna har ƙasa a gabansa,