2 Kings 2:4 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Iliya ya ce masa, “Ka dakata a nan Elisha; Ubangiji ya aike ni Yeriko.” Sai ya ce masa, “Muddin Ubangiji yana a raye, kai ma kana a raye, ba zan rabu da kai ba.” Saboda haka sai suka tafi Yeriko.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ إِلْيَاسُ يَثٜىٰ وَ أَلْيَسَعَ «إِنَ ضُواْڧُوانْكَ كَدَكَتَ أَنَنْ، غَمَا يَهْوٜىٰهْ يَثٜىٰ إِنْ تَڢِے يٜىٰرِكُواْ؞» عَمَّا أَلْيَسَعَ يَثٜىٰ «نَا ضَنْڟٜىٰ دَ سُونَنْ يَهْوٜىٰهْ مَيْ رَيْ دَ كُمَ رَنْكَ ثٜىٰوَ بَذَنْبَرْ كَبَ؞» سَيْ سُكَ تَڢِے يٜىٰرِكُواْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan Iliya ya ce masa, “Elisha, ina roƙonka ka dakata a nan gama Ubangiji ya aike ni Yariko.” Amma Elisha ya ce, “Na rantse da Ubangiji da kuma kai kanka, ba zan rabu da kai ba.” Sai suka tafi Yariko.