2 Kings 2:5 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ƙungiyar annabawa a Yeriko suka haura zuwa wajen Elisha suka ce, “Ko ka san Ubangiji zai ɗauki maigidanka daga gare ka yau?” Sai ya ce, “I, na sani, amma ku bar zancen nan tukuna.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ وَتَ ڧُنْ‌غِيَرْ أَنَّبَاوَنْ دَسُكٜىٰ دَ ذَمَ أَ يٜىٰرِكُواْ سُكَ تَڢِے وُرِنْ أَلْيَسَعَ سُكَ تَمْبَيٜىٰشِ سُكَثٜىٰ «كُواْ كَاسَنِ ثٜىٰوَ يَوْ نٜىٰ يَهْوٜىٰهْ ذَيْ طَوْكِ شُوغَبَنْكَ دَغَ غَرٜىٰكَ؟» أَلْيَسَعَ يَأَمْسَ يَثٜىٰ «عِ، نَا سَنِ؞ كُواْوَ يَيِ شِضُ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ƙungiyar annabawa da take Yariko suka zo wurin Elisha suka ce masa, “Ko ka sani yau Ubangiji zai ɗauke maigidanka?” Ya ce, “Na sani, amma mu bar zancen tukuna.”