2 Kings 20:19 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Hezekiya ya ce, “Maganar Ubangiji da ka faɗa ta yi kyau.” Gama ya yi tunani cewa, “Ai, ba ni da damuwa, tun da yake za a yi zaman lafiya da salama a kwanakina.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً هٜىٰزٜىٰكِيَ يَثٜىٰوَ أَنَّبِے عِشَايَ «مَغَنَرْ يَهْوٜىٰهْ وَدَّ كَكَٰوُاْ مِنِ تَنَدَ ݣَوْ؞» غَمَا يَنَ تُنَانِ ثٜىٰوَ «أَيْ، بَانِدَ دَامُوَ، تُنْدَيَكٜىٰ ذَاعَيِ ذَمَنْ لَاڢِيَ دَ سَلَمَ عَݣُونَكِنَ!»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sarki Hezekiya kuwa ya fahimci za a yi zaman lafiya da salama a zamaninsa, don haka ya amsa ya ce, “Jawabin da ka kawo mini daga wurin Ubangiji yana da kyau.”