2 Kings 21:13 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zan auna Urushalima da ma’aunin da na yi amfani da shi a kan Samariya, zan kuma yi amfani da magwajin da na yi amfani da shi a kan gidan Ahab. Zan shafe Urushalima yadda mutum yake wanke kwano yă kife.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً ذَنْ عَوْنَ إِسْرَٰٓءِيلَ دَ إِرِنْ إِغِيَرْ أَوُانْ هَلَّكَرْدَ نَيِ أَمْڢَانِ دَ عِتَ عَكَنْ سَمَرِيَ دَ كُمَ وَدَّ نَيِ أَمْڢَانِ دَ عِتَ عَكَنْ غِدَنْ أَهَبْ؞ ذَنْ لَشٜىٰ عُرُوشَلِيمَ كَمَرْ يَدَّ مُتُمْ يَكَنْ لَشٜىٰ ݣُونُواْ يَكِڢٜىٰشِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Zan gwada Urushalima da magwajin Samariya da kuma ma'aunin gidan Ahab. Zan kuma suɗe Urushalima kamar yadda mutum yakan suɗe akushi sa'an nan ya kifar da shi.