2 Kings 21:24 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai mutanen ƙasar suka kashe duk waɗanda suka ƙulla wa Sarki Amon maƙarƙashiya, sa’an nan suka naɗa ɗansa sarki a maimakonsa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا مُتَنٜىٰنْ ڧَسَرْ سُكَ كَشٜىٰ دُكَنْ وَطَنْدَ سُكَ كَشٜىٰ سَرْكِے أَمُوانْ؞ سَيْ سُكَ مَيْدَ طَنْسَ يُواْسِيَا سَرْكِے أَمَيْمَكُوانْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma mutanen ƙasar suka kashe waɗannan da suka yi wa sarki Amon maƙarƙashiyar. Sai suka naɗa Yosiya ɗan sarki, ya gāji tsohonsa.