2 Kings 21:3 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ya sāke gina masujadan da mahaifinsa Hezekiya ya rurrushe. Ya kuma gina wa Ba’al bagadai. Ya kafa ginshiƙin Ashera kamar yadda Ahab sarkin Isra’ila ya yi. Ya durƙusa wa dukan rundunan taurari ya yi musu sujada.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَرْكِے مَنَسّٜىٰ يَسَاكٜىٰ غِنَا وَطَنْسُ وُرَارٜىٰنْ سُجَّدَ دَ بَسُ دَاثٜىٰبَ، وَطَنْدَ بَابَنْسَ سَرْكِے هٜىٰزٜىٰكِيَ يَرُرُّشٜىٰ؞ يَكُمَ غِنَا بَغَدَيْ دُواْمِنْ غُنْكِنَّنْ بَعَلْ، يَكُمَيِ غُنْكِنْ أَشٜىٰرَ، كَمَرْ يَدَّ سَرْكِے أَهَبْ نَ إِسْرَٰٓءِيلَ يَيِ؞ يَكُمَيِ سُجَّدَ غَ رَانَ دَ وَتَ دَ تَوْرَرِنْ سَمَ يَنَ بَوْتَا مُسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Gama ya gina matsafai a kan tuddai waɗanda Hezekiya tsohonsa ya rurrushe. Ya kuma gina wa Ba'al bagadai, ya kuma yi gunkiyan nan, wato Ashtoret, kamar yadda Ahab, Sarkin Isra'ila, ya yi. Ya yi wa taurari sujada, ya bauta musu.