2 Kings 22:9 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan Shafan ya koma wurin sarki ya ce masa, “Hafsoshinka sun kwashe kuɗin da suke a haikalin Ubangiji, suka ba wa masu aiki da masu lura da haikalin.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً شَڢَنْ مَرُبُوثِنْ يَتَڢِے وُرِنْ سَرْكِے يَڢَطَا مَسَ يَثٜىٰ «رَنْكَيَدَطٜىٰ، مَاسُ عَيْكِنْكَ سُنْ ݣُوشِ كُطِنْ دَ عَكَ تَارَ دَغَ ثِكِنْ غِدَنْ يَهْوٜىٰهْ ، سُكَ بَادَشِ غَ مَاسُ لُورَ دَ عَيْكِنْ ڠَرٜىٰ ڠَرٜىٰنْ غِدَنْ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Shafan magatakarda ya tafi ya faɗa wa sarki cewa, “Baranka ya kwashe kuɗin da ya tarar a Haikali, na kuwa ba masu lura da ma'aikatan Haikalin Ubangiji.”