2 Kings 23:12 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ya rushe bagadan da sarakunan Yahuda suka kafa a kan ɗakin sama kusa da ɗakin sama na Ahaz, da kuma bagadai biyu da Manasse ya gina a filaye biyu na haikalin Ubangiji. Ya kawar da su daga can, ya farfashe su, ya zubar da tarkacen a Kwarin Kidron.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَرَاكُنَنْ يَهُودَ سُنْ غِنَا بَغَدَيْ عَكَنْ رُڢِنْ غِدَنْ سَرْكِے أَهَظْ؞ أَݣَويْ كُمَ بَغَدَيْ أَ ڢِيلَيٜىٰ بِيُ نَثِكِنْ غِدَنْ يَهْوٜىٰهْ ، وَطَنْدَ سَرْكِے مَنَسّٜىٰ يَغِنَ؞ دُكَنْ وَطَنَّنْ بَغَدَيْ سَرْكِے يُواْسِيَا يَتُورَسُ ڧَسَا يَڢَرْڢَشٜىٰسُ يَوَاڟَرْ دَسُو أَ ݣُورِنْ كِدْرُوانْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya rurrushe, ya kuma farfasa bagaden da yake bisa rufin benen Ahaz, waɗanda sarakunan Yahuza suka gina, da kuma bagaden da Manassa ya gina a farfajiya biyu ta Haikalin Ubangiji. Sai ya watsar da tokar da ƙurar a rafin Kidron.