2 Kings 23:16 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da Yosiya ya dubi kewaye da shi, ya ga kaburburan da suke can a gefen tudu, sai ya sa aka kwaso ƙasusuwan da suke cikinsu aka ƙone a kan bagade don yă lalatar da shi bisa ga maganar Ubangiji ta bakin mutumin Allah, wanda ya yi annabcin waɗannan abubuwa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَ سَرْكِے يُواْسِيَا يَجُويَ كَنْسَ، سَيْ يَغَ وَطَنْسُ كَبَرِ عَكَنْ تُدُنْ دَيَكٜىٰ ڟَيٜىٰ؞ سَيْ يَعَيْكَ عَكَ تُواْنَ ڧَسُسُوَنْ، عَكَ ڧُواْنٜىٰسُ عَكَنْ بَغَدٜىٰنْ؞ تَهَكَ عَكَ ڧَظَنْتَرْ دَ بَغَدٜىٰنْ؞ وَنَّنْ يَثِكَ مَغَنَرْ يَهْوٜىٰهْ وَدَّ مُتُمِنْ اللَّهْ يَيِ أَنَّبْثِ ثٜىٰوَ أَبُبُوَنَّنْ ذَاسُ ڢَرُ حَكَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da Yosiya ya waiwaya, sai ya ga kaburbura a kan dutse. Ya aika a kwaso ƙasusuwan da suke cikin kaburburan, sai ya ƙone su a bisa bagaden, ya lalatar da shi kamar yadda Ubangiji ya faɗa ta bakin annabi.