2 Kings 23:19 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kamar yadda ya yi a Betel, Yosiya ya kawar da dukan ɗakunan gumaka a kan tuddan da sarakunan Isra’ila suka gina a garuruwan Samariya, waɗanda suka tozarta Ubangiji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَنْدَ حَكَمَا سَرْكِے يُواْسِيَا يَكَوَرْدَ دُكَنْ طَكُنَنْ ڟَاڢِ أَوُرَارٜىٰنْ سُجَّدَ دَ بَسُ دَاثٜىٰبَ وَطَنْدَ سُكٜىٰ عَبِرَنٜىٰنْ سَمَرِيَ، وَطَنْدَ سَرَاكُنَنْ إِسْرَٰٓءِيلَ سُكَ غِنَا؞ تَهَكَ سُكَسَا يَهْوٜىٰهْ يَيِ ڢُشِے؞ سَرْكِے يُواْسِيَا يَايِ وَطَكُنَنْ ڟَاڢِنَّنْ دَيْدَيْ يَدَّ يَيِ أَ بٜىٰتٜىٰلْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Dukan matsafai na kan tuddai da suke a garuruwan Samariya waɗanda sarakunan Isra'ila suka gina, har suka sa Ubangiji ya yi fushi, Yosiya ya watsar da su. Ya yi da su kamar yadda ya yi a Betel.