2 Kings 23:36 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yehohiyakim yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekara goma sha ɗaya a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Zebuda ’yar Fedahiya, mutuniyar Ruma.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يٜىٰهُواْيَكِمْ يَنَدَ شٜىٰكَرَا عَشِرِنْ دَ بِيَرْدَ يَڢَارَ مُلْكِ؞ يَيِ مُلْكِ أَ عُرُوشَلِيمَ شٜىٰكَرَا غُواْمَشَا طَيَ؞ سُونَنْ مَامَرْسَ ظٜىٰبِدَ، یَرْ ڢٜىٰدَيَ مُتُمِنْ رُمَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yehoyakim yana da shekara ashirin da biyar sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi mulki shekara goma sha ɗaya a Urushalima. Sunan tsohuwarsa kuwa Zebida, 'yar Fediya mutumin Ruma.