2 Kings 23:9 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ko da yake firistocin masujadan kan tuddai ba su yi hidima a bagaden Ubangiji a Urushalima ba, sun ci burodi marar yisti tare da sauran firistoci.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَعَيَرْدَ وَڢِرِسْتُواْثِے نَوُرَارٜىٰنْ سُجَّدَ دَ بَسُ دَاثٜىٰبَ سُيِ حِدِمَ عَكَنْ بَغَدٜىٰنْ يَهْوٜىٰهْ أَ عُرُوشَلِيمَ بَ، عَمَّا سُنَ عِيَ ثِنْ غُرَاسَرْ مَرَرْ يِسْتِ تَرٜىٰدَ سَوْرَنْ ڢِرِسْتُواْثِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Duk da haka firistoci matsafai na kan tuddai ba su haura zuwa bagaden Ubangiji a Urushalima ba, amma suka ci abinci marar yisti tare da 'yan'uwansu.