2 Kings 24:15 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Nebukadnezzar ya ɗauki Yehohiyacin ya kai bauta a Babilon. Ya kuma kwashe mahaifiyar sarki, da matansa, da fadawansa, da manyan mutanen ƙasar daga Urushalima ya kai Babilon.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
نٜىٰبُكَدْنٜىٰزَّرْ يَطَوْكِ يٜىٰهُواْيَكِنْ ذُوَا بَابِيلَ، تَرٜىٰدَ سَرَوْنِيَ مَامَرْسَ دَ مَاتَنْسَ دَ دَتَّاوَنْسَ دَ مَنْيَنْ مُتَنٜىٰنْ ڧَسَرْ؞ دُكَ يَݣُوشٜىٰسُ ذُوَا بَوْتَا عَ بَابِيلَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya tafi da Yekoniya a Babila, shi da tsohuwarsa, da fādawansa, da masu maƙami na ƙasar.