2 Kings 24:20 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda fushin Ubangiji ne dukan waɗannan abubuwa suka faru da Urushalima, da kuma Yahuda, a ƙarshe kuma ya kawar da su daga fuskarsa. To, sai Zedekiya ya yi wa sarkin Babilon tawaye.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
حَڧِيڧَ مُتَنٜىٰنْ عُرُوشَلِيمَ دَ نَ يَهُودَ سُنْ سَا يَهْوٜىٰهْ يَا يِڢُشِے سُواْسَيْ، حَرْ يَكَوَرْ دَسُو دَغَ ڢُسْكَرْسَ؞ ﴿شٜىٰكَرَا 587 كَاڢِنْ حَيْڢُوَرْ عِيسَىٰ ﴾ سَعَنً صَدِڧِيَ يَيِ وَسَرْكِنْ بَابِيلَ تَاوَيٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji kuwa ya husata ƙwarai da mutanen Urushalima da dukan mutanen Yahuza, sai ya kore su daga gabansa. Zadakiya kuwa ya tayar wa Sarkin Babila.