2 Kings 25:1 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A rana ta goma ga wata na goma, a shekara ta tara ta mulkin Zedekiya ne Nebukadnezzar sarkin Babilon tare da dukan rundunan yaƙinsa, ya tasam wa Urushalima. Ya yi sansani a bayan birnin, ya kewaye ta da shirin yaƙi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَنَانً أَ شٜىٰكَرَا تَتَرَ تَمُلْكٍ سَرْكِے صَدِڧِيَ، أَ رَانَ تَغُواْمَ غَ وَتَنْ غُواْمَ، سَيْ سَرْكِے نٜىٰبُكَدْنٜىٰزَّرْ نَ بَابِيلَ يَذُواْ دَ دُكَنْ سُواْجُواْجِنْسَ دُواْمِنْ يَاڧِ دَ عُرُوشَلِيمَ؞ يَكٜىٰوَيٜىٰ بِرْنِنْ دُواْمِنْ يَاڧِ، يَكُمَ تَادَ أَبُبُوَنْ هَوْرَ كَتَنْغَ دُواْمِنْ يَاڧِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A shekara ta tara ta sarautar Zadakiya a kan rana ta goma ga watan goma, sai Nebukadnezzar Sarkin Babila, tare da sojojinsa, ya kawo wa Urushalima yaƙi. Suka kewaye ta da yaƙi, suka gina mata kagarai.