2 Kings 25:17 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Tsawon kowane ginshiƙi, ƙafa ashirin da bakwai ne. Hulunan tagullan da suke ƙwalƙwalin kowane ginshiƙi kuma yana da tsawon ƙafa huɗu da rabi. Kuma aka yi masa ado da saƙa da ’ya’yan itace kewaye da shi. Bayan ginshiƙin ma haka yake.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كُواْوَنٜىٰ غِنْشِڧِ ڟَيِنْسَ يَيِ ڧَڢَا عَشِرِنْ دَ بَݣَويْ، كَنْسَ نَتَغُلَّ كُمَ يَيِ ڧَڢَا حُطُ دَ رَبِے؞ كُواْوَنٜىٰ كَنْ غِنْشِڧِنْ يَنَدَ أَدُوانْ ذَانِ ذَانِنْ رَاغَرْ سَرْڧَ دَ نَیَیَنْ رُمَّنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Tsayin kowane ginshiƙi kamu goma sha takwas ne. A kan kowane ginshiƙi akwai dajiyar tagulla, wadda tsayinta ya kai kamu uku. Akwai raga da rumman na tagulla kewaye da dajiyar.