2 Kings 25:19 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Daga cikin waɗanda suka rage a birnin, ya ɗauki hafsa mai kula da dakaru, da kuma mashawartan sarki guda biyar. Ya kuma tafi da magatakarda wanda yake babban jami’in soja mai ɗaukan dukan jama’an ƙasar, tare da mutanensa guda sittin waɗanda aka samu a birnin.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَغَ مُتَنٜىٰنْ دَ حَرْ يَنْذُ سُنَ ثِكِنْ بِرْنِنْ، يَطَوْكِ وَنِ شُوغَبَنْ سُواْجُواْجِ دَ دَتَّاوَا بِيَرْ نَسَرْكِے؞ يَكُمَ طَوْكِ مَرُبُوثِ نَشُوغَبَنْ سُواْجُواْجِنْ ڧَسَرْ وَنْدَ يَكٜىٰ طَوْكَرْ مُتَنٜىٰ أَ عَيْكِنْ سُواْجَ، تَرٜىٰدَ وَطَنْسُ مُتَنٜىٰ سِتِّنْ دَ عَكَ سَامُ عَثِكِنْ بِرْنِنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Daga cikin birnin kuma ya tafi da wani shugaban sojoji, da 'yan majalisar sarki mutum biyar, da magatakardan shugaban sojoji wanda ya tattara jama'ar ƙasar, da mutum sittin na ƙasar waɗanda aka samu a birnin.