2 Kings 25:4 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai aka huda katanga sa’an nan dukan sojoji suka tsere da dare a ƙofa tsakanin katanga biyu da suke kusa da lambun sarki, ko da yake Babiloniyawa sun kewaye birnin. Suka tsere suka nufi Araba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ عَكَ ڢَسَ وَنِ سَاشٜىٰ نَكَتَنْغَرْ بِرْنِنْ؞ سَيْ دُكَنْ سُواْجُواْجِنْ سُكَ غُدُ دَ دَرٜىٰ تَوُرِنْ ڧُواْڢَرْ دَتَكٜىٰ ڟَكَانِنْ بَنْغُواْ بِيُ، وَدَّ تَكٜىٰ كُسَدَ غُواْنَرْ سَرْكِے؞ سَعَدَّ سُواْجُواْجِنْ بَابِيلَ سُنَ كٜىٰوَيٜىٰ دَ بِرْنِنْ، سَرْكِے صَدِڧِيَ دَ سُواْجُواْجِنْسَ سُكَ غُدُ ذُوَا تَݣُورِنْ يُواْدَنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai aka huda garun birnin, sarki da mayaƙa suka tsere da dare ta hanyar ƙofar da take tsakanin bango biyu kusa da gonar sarki, suka bi ta hanyar Araba, ko da yake Kaldiyawa suna kewaye da birnin.