2 Kings 3:1 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yoram, ɗan Ahab ya zama sarki Isra’ila, a Samariya, a shekara ta goma sha takwas ta mulkin Yehoshafat, sarkin Yahuda, ya kuma yi mulki shekara goma sha biyu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَ شٜىٰكَرَا تَغُواْمَشَا تَݣُوسْ تَمُلْكٍ سَرْكِے يٜىٰهُواْشَڢَتْ نَ يَهُودَ، يٜىٰهُواْرَمْ طَنْ أَهَبْ يَذَمَ سَرْكِنْ إِسْرَٰٓءِيلَ أَ سَمَرِيَ؞ يٜىٰهُواْرَمْ يَيِ مُلْكِ شٜىٰكَرَا غُواْمَشَا بِيُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A shekara ta goma sha takwas ta sarautar Yehoshafat Sarkin Yahuza, Yehoram ɗan Ahab ya zama Sarkin Isra'ila a Samariya. Ya yi mulki shekara goma sha biyu.