2 Kings 3:12 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yehoshafat ya ce, “Maganar Ubangiji tana tare da shi.” Saboda haka sarkin Isra’ila da Yehoshafat da kuma sarkin Edom suka tafi wurin Elisha.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يٜىٰهُواْشَڢَتْ يَثٜىٰ «كَلْمَرْ يَهْوٜىٰهْ تَنَ تَرٜىٰ دَشِ؞» دُواْمِنْ حَكَ سَرْكِنْ إِسْرَٰٓءِيلَ دَ سَرْكِنْ يَهُودَ دَ سَرْكِنْ عٜىٰدُوامْ سُكَ تَڢِے وُرِنْ أَلْيَسَعَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yehoshafat kuwa ya ce, “Gaskiya ne, maganar Ubangiji tana tare da shi.” Saboda haka sai sarakunan nan uku suka ɗunguma zuwa wurin Elisha.