2 Kings 3:19 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Za ku ci kowane birni mai katanga, da kowane babban gari. Za ku sare kowane itace mai kyau, ku kuma tattoshe maɓuɓɓugan ruwa. Za ku kuma yi amfani da duwatsu ku lalatar da kowace gona mai kyau.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَاكُ ڨُوثٜىٰ كُواْوَنٜىٰ بِرْنِ مَيْ كَتَنْغَ دَ كُواْوَنٜىٰ بِرْنِ مَيْݣَوْ؞ ذَاكُ يَنْكَ كُواْوَنٜىٰ إِتَاثٜىٰ مَيْ أَمْڢَانِ، ذَاكُ تُواْشٜىٰ كُواْوَثٜىٰ مَٻُٻُّغَرْ ضُوَنْسُ، كُمَ دَ دُوَڟُو ذَاكُ لَلَتَرْدَ غُواْنَكِنْسُ مَاسُ ݣَوْ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Za ku ci kowane birni mai garu da kowane birni na musamman. Za ku sassare kowane kyakkyawan itace, ku kuma tattoshe maɓuɓɓugan ruwa. Za ku lalatar da gonaki masu kyau da duwatsu.”