2 Kings 3:25 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Suka ragargaza garuruwa, kowane mutum kuwa ya jefa dutse a kowane gona mai kyau har sai da aka rufe gonakin gaba ɗaya. Suka tattoshe duk maɓulɓulan ruwa, suka kuma sare duk itace mai kyau. Kir Hareset ne kaɗai aka bari tare da duwatsunsa yadda suke, amma mutanen da suke da majajjawa suka yi wa birnin zobe, suka kai masa hari shi ma.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سُكَ لَلَتَرْدَ بِرَنٜىٰنْسُ؞ عَكُواْوَثٜىٰ غُواْنَ مَيْݣَوْ، كُواْوَ يَجٜىٰڢَ دُوڟٜىٰ عَثِكِ حَرْ سَيْ دَ أَنْرُڢٜىٰتَ دَ دُوَڟُو؞ عَكَ تُواْشٜىٰ كُواْوَثٜىٰ مَٻُٻُّغَرْ ضُوَ، عَكَ كُمَ يَنْكَ كُواْوَنٜىٰ إِتَاثٜىٰ مَيْ أَمْڢَانِ؞ عَڧَرْشٜىٰ بَبَّنْ بِرْنِنْسُ كِرْ هٜىٰرٜىٰسٜىٰتْ كَطَيْ يَرَغُ، عَمَّا سُواْجُواْجِ مَاسُ مَجَجَّوَ سُكَ كٜىٰوَيٜىٰشِ سُكَ ڢَاطَ مَسَ دَيَاڧِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
suka lalatar da biranensu, a kowace kyakkyawar gona kuma, kowannensu ya jefa dutse a cikinta, har aka cika ta da duwatsu, suka kuma tattoshe kowace maɓuɓɓugar ruwa, suka sassare kyawawan itatuwa. Babban birnin Kir-hareset kaɗai ya ragu, Isra'ilawa suka kewaye shi suka fāɗa shi da yaƙi.