2 Kings 3:4 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Mesha, sarkin Mowab yana kiwon tumaki, ya kuma zama tilas yă biya haraji ga sarkin Isra’ila. Saboda haka yakan ba da ’yan tumaki dubu ɗari, da kuma gashin raguna dubu ɗari.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَرْكِے مٜىٰشَ نَ مُواْوَبْ كُوَ مَكِيَايِنْ تُمَكِ نٜىٰ؞ كُواْوَثٜىٰ شٜىٰكَرَا يَكَنْ بَا سَرْكِنْ إِسْرَٰٓءِيلَ هَرَاجِ نَیَنْ تُمَكِ دُبُو طَرِے دَ غَاشِ دَغَ رَغُنَ دُبُو طَرِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Mesha Sarkin Mowab kuwa makiyayin tumaki ni. Yakan ba Sarkin Isra'ila 'yan tumaki dubu ɗari (100,000), da raguna dubu ɗari (100,000) duk da ulunsu, gandu a shekara.