2 Kings 3:7 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ya kuma aika da wannan saƙo ga Yehoshafat sarkin Yahuda cewa, “Sarkin Mowab ya yi mini tawaye. Za ka tafi tare da ni mu yaƙi Mowab?” Sai sarkin Yahuda ya ce, “I, ina shirye mu tafi. Ai, sojojina sojojinka ne, dawakaina kuma dawakanka ne.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَعَيْكَ دَسَڧُواْ ذُوَا سَرْكِے يٜىٰهُواْشَڢَتْ نَ يَهُودَ يَثٜىٰ «سَرْكِنْ مُواْوَبْ يَيِ مِنِ تَاوَيٜىٰ؞ كُواْ ذَاكَ تَڢِے دَنِے مُيَاڧِ مُواْوَبْ؟» يٜىٰهُواْشَڢَتْ يَأَمْسَ يَثٜىٰ «عِ، إِنَ شِرْيٜىٰ مُتَڢِے؞ أَيْ، سُواْجُواْجِنَ سُواْجُواْجِنْكَ نٜىٰ دَوَكِنَ كُمَ دَوَكِنْكَ نٜىٰ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya kuma aika wa Yehoshafat Sarkin Yahuza, ya ce, “Sarkin Mowab ya tayar mini, ko za ka yarda ka tafi tare da ni mu yaƙi Mowabawa?” Yehoshafat ya ce, “Zan tafi, ni kamarka ne, mutanena kuma kamar mutanenka, dawakaina kuma kamar naka.