2 Kings 4:13 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Elisha ya ce masa, “Ka ce mata, ‘Kin yi duk wannan ɗawainiya saboda mu. Yanzu, me kike so a yi miki? Kina so mu yi magana a madadinki wa sarki ko babban hafsan mayaƙa?’ ” Sai ta ce, “A’a, ina da dukan abin da nake bukata a cikin jama’ata.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَلْيَسَعَ يَغَيَ وَ غٜىٰهَظِ يَڢَطَا مَتَ ثٜىٰوَ «دَيَكٜىٰ كِنْدَامُ دَمُو حَرْ كِنْيِ مَنَ دُكَنْ أَلْحٜىٰرَنَّنْ، مٜىٰ كِكٜىٰسُواْ عَيِمِكِ؟ كِنَ سُواْ عَيِ وَسَرْكِے مَغَنَ كُواْ كُوَ عَيِ وَشُوغَبَنْ سُواْجُواْجِ مَغَنَ؟» تَا أَمْسَ تَثٜىٰ «أَعَ، إِنَ تَرٜىٰدَ مُتَنٜىٰنَ، بَانَ بُڧَاتَرْ كُواْمٜىٰ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya ce wa Gehazi, “Ka tambaye ta me take so in yi mata saboda dukan wannan wahala da ta yi dominmu? Tana so in yi mata magana da sarki ko da shugaban sojoji?” Sai ta ce, “Ai, ina da dukan abin da nake bukata a cikin jama'ata.”