2 Kings 4:34 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan ya hau gadon yă kwanta a bisa yaron, ya miƙe a kansa, baki da baki, ido da ido, hannu da hannu. Yayinda ya miƙe kansa a kan yaron, sai jikin yaron ya ɗau ɗumi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً يَݣُونْتَ عَكَنْ جِكِنْ يَرُوانْ؞ يَسَا بَاكِنْسَ عَكَنْ بَاكِنْ يَرُوانْ، حَكَمَا عِدَنُونْسَ أَعِدَانُنْ يَرُوانْ دَ كُمَ حَنُّوَنْسَ عَكَنْ حَنُّوَنْ يَرُوانْ؞ دَيَمِيڧٜىٰ كَنْسَ عَكَنْ يَرُوانْ، سَيْ جِكِنْ يَرُوانْ يَيِ طُمِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan ya kwanta a kan yaron, ya sa bakinsa a bakin yaron, ya sa idanunsa a idanun yaron, hannuwansa kuma a kan na yaron, ya miƙe jikinsa akan yaron, sai jikin yaron ya yi ɗumi.