2 Kings 4:39 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ɗaya daga cikin mutanen ya shiga gona don neman ganyaye, ya kuwa sami kabewar jeji. Ya tsinko ’ya’yanta cike da shafin rigarsa. Da ya dawo, sai ya yayyanka su ya zuba a cikin tukunyar faten, ko da yake ba wanda ya san ko mene ne.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
طَيَ دَغَ ثِكِنْ مَاسُ حِدِمَرْ يَشِغَ دَاجِ دُواْمِنْ يَسَامُواْ غَنْيَيٜىٰ نَثِ؞ سَيْ يَسَامِ كَبٜىٰوَرْ دَاجِ، يَطٜىٰبُواْ یَیَنْتَ يَرِڧٜىٰ أَ رِغَرْسَ يَكَٰوُاْ غِدَا؞ يَيَيَّنْكَ يَظُبَ عَتُكُنْيَرْ عَبِنْثِنْ بَاتَرٜىٰدَ سَنِ كُواْ مٜىٰنٜىٰنٜىٰبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ɗaya daga cikinsu ya tafi saura don ya samo ganyayen ci. Sai ya ga yaɗon inabin jeji, ya ɗebo 'ya'yan ya rungumo cike da hannu, ya zo ya yanyanka ya zuba a tukunyar abinci, ba tare da sanin ko mene ne ba.