2 Kings 4:5 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ta tashi ta shiga tare da ’ya’yanta maza, suka kulle ƙofa. ’Ya’yanta suka kawo mata tuluna, ita kuma tana ɗurawa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مَثٜىٰنْ كُوَ تَتَڢِے؞ سَيْ تَشِغَ طَاكِ تَرٜىٰدَ یَیَنْتَ مَظَا، سُكَ كُلّٜىٰ ڧُواْڢَرْ؞ سَيْ تَڢَارَ جُويٜىٰ مَنْ ظَيْتُنْ طِنْ، یَیَنْتَ سُنَ تَكَٰوُاْ مَتَ تُلُنَ، عِتَ تَنَ تَجُويٜىٰ مَيْ عَثِكِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai ta tashi daga wurinsa, ta tafi ta shiga ɗaki tare da 'ya'yanta, ta rufe ƙofar. 'Ya'yan suna kawo tandaye tana ɗurawa.