2 Kings 4:7 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai ta tafi ta faɗa wa mutumin Allah. Shi kuwa ya ce mata, “Tafi, ki sayar da man, ki biya bashinki. Ki biya bukatanki da na ’ya’yanki da sauran da ya rage.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
تَا تَڢِے تَڢَطَا وَ أَلْيَسَعَ مُتُمِنْ اللَّهْ ، سَيْيَثٜىٰ مَتَ «كِتَڢِے كِسَيَرْ دَ مَنْ، كِبِيَ بَاشِنْكِ، سَعَنً كٜىٰ دَ یَیَنْكِ ذَاكُ عِيَ رَايُ عَكَنْ أَبِنْدَ يَرَغُ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai ta koma ta faɗa wa annabi Elisha, shi kuwa ya ce mata, “Ki je ki sayar da man, ki biya bashin, abin da ya ragu kuwa ki ci, ke da 'ya'yanki.”