2 Kings 5:1 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Na’aman babban hafsan hafsoshin rundunar sarkin Aram ne, kuma ƙasaitaccen mutum ne mai martaba a idon maigidansa, domin ta wurinsa Ubangiji ya ba Aram nasara. Na’aman jarumi ne ƙwarai, amma yana da kuturta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
نَعَمَنْ كُوَ شُوغَبَنْ سُواْجُواْجِنْ سَرْكِنْ سُورِيَ؞ سَرْكِنْ سُورِيَ يَنَ غِرْمَمَ شِ يَنَ كُمَ جِنْ دَاطِنْسَ ڨُورَيْ، دُواْمِنْ تَهَنُّنْسَ نٜىٰ يَهْوٜىٰهْ يَبَا سُرِيَاوَا نَصَرَا؞ شِ سُواْجَ مَيْ عِيَ يَاڧِ نٜىٰ، عَمَّا يَنَدَ ثُوتَرْ ڢَتَرْ جِكِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Na'aman kuwa, shugaban sojojin Sarkin Suriya, shi babba ne mai farin jini ƙwarai a wurin ubangidansa, domin ta wurinsa ne Ubangiji ya ba Suriyawa nasara. Shi mutum ne ƙaƙƙarfan jarumi, amma kuma kuturu ne.