2 Kings 5:10 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Elisha ya aika ’yan saƙo su ce masa, “Je, ka nutse sau bakwai a Urdun, fatar jikinka za tă koma daidai, ka kuma tsarkaka.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَلْيَسَعَ يَعَيْكَرْ دَ طَنْ عَيْكَ يَثٜىٰ وَ نَعَمَنْ يَجٜىٰ كُواْغِنْ يُواْدَنْ يَنُڟٜىٰ سَوْ بَݣَويْ ثِكِنْ ضُوً، ڢَتَرْ جِكِنْسَ ذَيْ كُوَ وَرْكٜىٰ يَذَمَ لَاڢِيَيّٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Elisha ya aiki manzo ya faɗa wa Na'aman ya tafi, ya yi wanka a Kogin Urdun har sau bakwai, naman jikinsa zai warke, zai tsarkaka.