2 Kings 5:16 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Annabin ya amsa ya ce, “Muddin Ubangiji wanda nake bauta masa yana a raye, ba zan karɓi kome ba.” Ko da yake Na’aman ya yi ta roƙonsa, amma ya ƙi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَلْيَسَعَ يَأَمْسَ يَثٜىٰ «نَا ضَنْڟٜىٰ دَ سُونَنْ يَهْوٜىٰهْ مَيْ رَيْ، وَنْدَ نَكٜىٰ بَوْتَا مَسَ، بَذَنْ كَرْٻِ كُواْمٜىٰبَ؞» نَعَمَنْ يَمَاڟَ مَسَ يَكَرْٻَ، عَمَّا يَڧِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma Elisha ya ce, “Na rantse da Ubangiji, wanda nake bauta masa, ba zan karɓi kome ba.” Ya yi ta roƙonsa ya karɓa, amma ya ƙi.