2 Kings 5:23 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Na’aman ya ce, “Ba damuwa, karɓi talenti biyu.” Ya roƙi Gehazi yă karɓa, sa’an nan ya ƙunsa masa talentin biyu na azurfa ya sa masa a kan jakankuna biyu, ya haɗa da tufafi kashi biyu, ya ba bayinsa biyu suka ɗauka, ya ce su sha gaban Gehazi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
نَعَمَنْ يَأَمْسَ يَثٜىٰ «كَكَرْٻِ أَظُرْڢَا دُبُو شِدَ؞» نَعَمَنْ كُوَ يَمَاڟَ مَسَ يَكَرْٻِ أَظُرْڢَا دُبُو شِدَ، يَڧُنْسَ مَسَ عَثِكِنْ جَكَ بِيُ، تَرٜىٰدَ رِيغُنَ كَشِ بِيُ؞ يَ عُمَرْثِ بِيُ دَغَ یَنْ حِدِمَرْسَ سُكَ رِڧٜىٰوَ غٜىٰهَظِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Na'aman kuwa ya ce, “In ka yarda ka karɓi talanti biyu na azurfa.” Ya ƙirga su ya ɗaure kashi biyu, da kuma rigunan ado masu kyau ya ɗora wa barorinsa biyu, ya umarce su su kai wa Gehazi har gida.