2 Kings 5:24 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da Gehazi ya isa wani tudu, sai ya karɓi kayan daga wurin bayin ya shiga da su a ɓoye a cikin gida. Sa’an nan ya sallami mutanen suka tafi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَ سُكَ كَيْ كَنْ تُدُ كُسَدَ غِدَنْ أَلْيَسَعَ، سَيْ غٜىٰهَظِ يَكَرْٻَ، يَشِغَرْ دَسُو ثِكِنْ غِدَا؞ سَعَنً يَسَلَّمٜىٰسُ سُكَ كُواْمَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da Gehazi ya kai tudu, sai ya karɓi kayan daga hannunsu, ya ajiye a gida, sa'an nan ya sallame su, suka tafi.